Home / Zamfara in other media / Ban Auri ‘Yar shekara 13 ba- Yarima

Ban Auri ‘Yar shekara 13 ba- Yarima

A Najeriya tsohon gwamnan jihar Zamfara Sanata Ahmad Sani Yariman Bakura, ya mayar da martani a bisa zargin da kungiyoyin mata da na kare hakkin bil’adama suka yi masa abisa auren wata ‘yar kasar Masar da yayi.

A wata hira da yayi da wakilin BBC Jimeh Saleh ta wayar tarho, Sanatan yace auren da yayi bai sabawa tanade-tanaden addinin musulunci ba, abinda yasa yace bai damu da cece kucen da jama’a ke yi ba.
Sanata Yarama yace ba gaskiya bane zancen da ake na cewa matar da ya aura shekararta goma sha ukku.
Ya kara da cewa a matsayinsa na mai bin tsarin addinin musulunci sau da kafa, yasan wajibi ne ya fuskanci matsala a harkokin rayuwarsa.

Kungiyoyin na hadin gwiwa, wadanda suka hada da kungiyoyin mata daban-daban na kasar, da na lauyoyi da na likitoci, sun gabatar da korafi a gaban majalisar dattawa ta kasar ranar Laraba.
Suna cewar Sanata Yarima ya keta sashi na 21 na dokokin kare hakkin yara kanana da ta mata na majalisar dinkin duniya, da Najeriya ta sanyawa hannu.

To amma Sanata Ahmed Sani Yarima mai shekarun haihuwa arbain da tara, ya yi watsi da zargin da kungiyoyin suka yi masa yana mai cewa siyasa ce kawai da kuma bita da kulli, wacce yace ya saba fuskanta tun lokacin da ya kaddamar da aiki da tsarin shari’ar musulunci a jihar Zamfara a 1999.

To amma adai dai lokacin da Sanata Yarima ke cewa bai sabawa tsarin shari’ar musulunci ba, gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike akan zargin da ake yi ma tsohon gwamnan.
Gwamnatin ta ce duk da yake har yanzu bata tabbatar da zargin ba, ba za ta zura ido ta bari ana take hakkin mata ba, don haka za ta yi iyaka kokarinta wajen tabbatar da adalci.

Ministar harkokin mata da matasa, Mrs Josephine Aneneh ta ce idan har batun auren da ake zargin Sanata Ahmad Sanin ya yi ya tabbata gaskiya, to lallai za su umarci ministan shari’a ya shigar da kara a madadinsu, kamar yadda ta shaidawa Nasidi Adamu Yahaya.

To amma sai dai acewar malaman addinin musulunci, idan dai magana ce ta addini, to musulunci bai hana daura ma yarinya aure ba, muddum dai ba tilas ta mata akayi ba. Kamar yadda Ustaz Hussaini Zakariyya, wani malami a Abuja, ya shaidawa wakilin mu Ibrahim Mijinyawa. Daga Shafin BBc hausa

About IbrahimTuduBlog

Check Also

Zamfara bandits relocating to Katsina- Governor Masari

The governor made the call on Wednesday when the Emir of Katsina, Abdulmumini Kabir, paid him the traditional Sallah Homage.

%d bloggers like this:
Skip to toolbar